Nigerian news All categories All tags
Sojoji da masu bautar kasa sun mutu wajen rikicin Kabilanci a Kuros Riba

Sojoji da masu bautar kasa sun mutu wajen rikicin Kabilanci a Kuros Riba

Labari ya zo mana cewa a wancan makon ne mutum fiye da 200 su ka bakunci lahira a sanadiyyar rikicin kabilanci da ya barke a Garin Kuros-Riba da kuma Ebonyi da ke Kudancin Najeriya.

Sojoji da masu bautar kasa sun mutu wajen rikicin Kabilanci a Kuros Riba

Gwamna Dr. Ben Ayade na Jihar Kuros-Riba tare da Buhari

Jaridar Calabar Reporters ta rahoto cewa wani danyen rikici ne ya barke tsakanin ‘Yan kabilar Ukelle da ke Jihar Kuros Riba da kuma Mutanen Igbeabu na Jihar Ebonyi wanda ya ci mutum 210 wanda ciki har da Jami’an tsaro.

Kamar yadda mu ka samu labari an aika Jami’an Sojoji domin kwantar da hankali a Yankin inda Sojoji 4 su ka mutu nan-take daga isan su wurin. Daga cikin wasu da aka kashe kuma har da masu bautar kasa na NYSC a Yankin.

KU KARANTA: Za a fara jigilar alhazai zuwa Kasar Saudiyya

Bayan wannan mummunan hari da aka kai, Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi Dr. Kelechi Igwe ya fito yayi jawabi inda yace Gwamnati za tayi bakin kokari na ganin ta tsagaita wutan rikicin ta kuma hukunta wanda su kayi aikin.

Mutanen Ukelle da ke Yankin sun nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma sauran Jama’a har na kasashen waje su kawo masu agaji. Duk da Jami’an tsaro na Sojoji da ‘Yan Sanda da aka sa dai bai hana wannan kashe-kashe ba.

Kwanaki kun ji cewa wata mahaukaciyar tsawa ta yi sanadiyyar rushewar gidaje fiye da 100 a cikin Garin na Daura da ke cikin Jihar Katsina a daren Ranar Lahadi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel