Nigerian news All categories All tags
Buhari ya sanya dokar ta-baci kan cin-hanci

Buhari ya sanya dokar ta-baci kan cin-hanci

A yau, Alhamis, Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa dokar ta-baci kan cin hanci a Najeriya. Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya zata tabbatar cewa babu wani da zai yiwa doka zagon kasa musamman wanda ake tuhuma.

Buhari ya yi wannan maganar ne a yayin da yake rattaba hannu a kan wata doka da zata bawa gwamnati damar adana duk wata dukiya da aka sameta ta hanyar cin hanci kuma gwamnati ta kwace ta.

Ya saka hannu kan dokar ne a cikin dakin taron majalisar zartarwa dake fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Buhari ya sanya dokar ta-baci kan cin-hanci

Buhari ya sanya dokar ta-baci kan cin-hanci

Ya ce an kafa dokar ne saboda tabbatar da demokradiyar Najeriya da kuma habbaka tattalin arzikin kasa da kiyaye dukiyar kasar daga maciya amanan kasa kuma ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da sauran yan Najeriya su fara biyaya ga dokar.

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani basarake gaban a kuliya saboda magudin zabe

Ya kuma yi kira ga dukkan hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar Attoney Janar na kasa su tabbatar sun fara zartar da dokar tare koyi da ka'idojin aiki mafi kyawu a duniya.

"Dole dukkan yan Najeriya su hada karfi waje guda wajen fatatakar rashawa a duk inda take," inji shugaban kasar.

Ya bayyana cewa rattaba hannu kan dokar babbar nasara ce a yaki da rashawa da Najeriya keyi kuma dole ayi hakan idan har ana son a ci galabar rashawa a kasar.

Shugaban kasan kuma ya ce duk da cewa akwai dalilai masu yawa da ya janyo wa Najeriya koma baya rashawa ne ke kan gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel