Nigerian news All categories All tags
Buhari ya ki sahalewa bukatun Likitoci na baya-bayan nan

Buhari ya ki sahalewa bukatun Likitoci na baya-bayan nan

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi fatali da kudirin yiwa dokar ma'aikatan lafiya masu daukan hoto (Radiographers) gyara duk da cewa majalisa ta amince da kudirin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da rashin amincewa da kudirin ne a wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa Dr. Bukolar Saraki.

A wasikar da shugaban kasar ya aike a ranar 18 ga watan Yunin shekarar 2018, shiugaban kasan ya ce ya ki amincewa da dokar ne saboda sashi na 58(4) na kudin tsarin Najeriya.

Buhari ya ki sahalewa bukatun Likitoci na baya-bayan nan

Buhari ya ki sahalewa bukatun Likitoci na baya-bayan nan

A wasikar shugaban kasar ya bayyana cewa sanya hannu a dokar zai janyo rashin jituwa da rabuwan kawuna a fanin lafiya na kasar tsakanin masu daukan hoton cikin jikin dan adam (Radiographers) da kuma Likitoci da suka kware a fanin yin bayyani kan abinda hotunan ke nufi tare da bayar da magunguna na ciwon da aka gano.

DUBA WANNAN: Buhari ya sanya dokar ta-baci kan cin-hanci

Dama an dade ana samun sa-in-sa tsakanin Likitocin da kuma masu daukan hoton game da wasu abubuwa da ya shafi ayyukansu a asibitocin.

A wata wasikar kuma da shugaban kasar ya aike wa majalisa a ranar 19 ga watan Yunin 2018, shugaban kasar ya gabatar da kasafin kudin babban birnin tarayya Abuja ga majalisar kamar yadda sashi na 121 da 299 na kudin tsarin mulki ya tanadar.

Kazalika, a wata wasikar da shugaban kasar ya aike wa majalisar a ranar 8 ga watan Yuni, shugaba Buhari ya mika sunan Folashodun Adesbisi Shonubi a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin kasa CBN domin majalisar ta tattance shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel