Nigerian news All categories All tags
Da duminsa: Buhari ya yi doka a kan kadarorin gwamnati da aka kwato

Da duminsa: Buhari ya yi doka a kan kadarorin gwamnati da aka kwato

A yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammmadu Buhari ya saka hannu a kan wata doka da zata bawa gwamnati damar adana duk wata dukiya da aka sameta ta hanyar cin hanci kuma gwamnati ta kwace ta.

Ya saka hannu kan dokar ne a cikin dakin taron majalisar zartarwa dake fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Da yake ganawa da shugaban kasar Namibia, Hage Geingob, a jiya, Buhari ya bayyana shaida masa cewar, "lokacin da nake mulki a matsayin shugaban kasa na soji na kwace kadarorin masu cin hanci amma bayan an hambarar da gwamnatina sai aka mayar masu da dukiyoyinsu."

Buhari ya ce dukkan wata dukiya ko kadara da aka mallaketa ta hanyar cin hanci, za a kwace ta kuma a sayar a mayar da kudin lalitar gwamnati.

Da duminsa: Buhari ya yi doka a kan kadarorin gwamnati da aka kwato

Shugaba Buhari

Buhari ya mulki Najeriya a matsayin shugaban kasa na soji daga shekarar 1983 zuwa 1985. An zabe shi a matsayin shugaban kasa a mulkin dimokradiyya a shekarar 2015, yanzu kuma yana takarar neman a sake zabensa a karo na biyu a zaben da za a yi a shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Girma ya fadi: Yadda malamai ke cinye abincin daliban makarantun Firame a Kaduna

Tun bayan hawansa mulki a 2015, Buhari ya mayar da hankali a yaki da cin hanci da rashawa musamman ta hanyar binciken yadda gwamnatin da ya gada ta Jonathan ta kashe kudaden da ta fitar daga asusun gwamnatin tarayya da sunan yaki da aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram da ya lakume dubban rayukan 'yan Najeriya.

Wasu 'yan Najeriya, musamman bangaren jam'iyyar adawa ta PDP, na sukan yaki da cin hancin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi tare da bayyana cewar suna nuna wariya da son kai a kan wadanda ake tuhuma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel