Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya nada babban malami, Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan NCRI

Shugaba Buhari ya nada babban malami, Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan NCRI

Gwamnatin tarayya ta nada Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan ma’aikatar binciken irin abinci na kasa da ke Badeggi, jihar Neja.

Wannan labara ya samu ne a wasikar da diraktan harkokin jama’a na ma’aikatar noma da raya karkara, Mrs A. C Bawa a madadin ministan noma, Cif Audu Ogbeh.

Wani sashen wasikar tace: “Wannan nadi zai fara aiki ranan 2 ga watan Yuili kuma zai iya zama a kujerar har na tsawon shekaru 10 muddin baka isa shekarun ritaya ba bisa ga dokokin ma’aikatar.”

An nada Dakta Aliyu Umar ne bayan mutuwan tsohon shugaban cibiyar, Dr Samuel Agboireso, a ranan 7 ga watan Yuni, 2018.

An haifi Dakta Aliyu Umar a shekarar 1963 kuma ya fara aiki a ma’aikatar ne tun a matsayin karamin ma’aikaci har ya zama diraktan binciken waje.

Ya rike kujeran shugaban reshen Uyo, Akwa Ibom da Amakama, jihar Abiya a shekarun baya.

Ya samu kwalin doktoransa a ilimin kimiyar kasan noma daga jami’ar fasaha na Minna wato FUT Minna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel