Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

Sabon zababben shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamrad Adams Aliyu Oshiomhole na cikin ganawar sirri da masu ruwa da tsakin APC na majalisar wakilai a yanzu haka.

Oshiomhole wanda ya isa dakin ganawar, a majalisar dokoki da misalin karfe 3:00 na rana, ya samu rakiyan kakakin majalisar wakilai da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da Femi Gbajabiamila.

Zuwa yanzu ba’a sanar da jama’a dalilin ganawar ba amma dai majiyoyi sun bayyana cewa ba lallai ne ya kasance yana da nasaba da rikicin jam’iyya ba.

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Manyan sanatoci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All progressives Congress (APC) sun yi ganawa mai muhimmancin da kwamitin aikin jam’iyyar na kasa.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada babban malami, Dakta Aliyu Umar, a matsayin diraktan NCRI

Sun gana ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli duk da cewar ba’a bayyanawa jama’a cikakken bayanin ganawar ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel