Nigerian news All categories All tags
A daina alakanta ni da sabuwar PDP Ko sabuwar APC, Ina nan daram a cikin tsohuwar APC - Gwamna Tambuwal

A daina alakanta ni da sabuwar PDP Ko sabuwar APC, Ina nan daram a cikin tsohuwar APC - Gwamna Tambuwal

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya nisanta kansa daga zargin da ake masa na shirin barin jam’iyyar APC mai mulki.

Rariya ta ruwaito cewa Gwamnan ya ce a daina alakanta shi da sabuwar PDP ko sabuwar APC, cewa yana nan har yanzu a tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

A daina alakanta ni da sabuwar PDP Ko sabuwar APC, Ina nan daram a cikin tsohuwar APC - Gwamna Tambuwal

A daina alakanta ni da sabuwar PDP Ko sabuwar APC, Ina nan daram a cikin tsohuwar APC - Gwamna Tambuwal

Gwamnan na cewa: “A daina alakanta ni da sabuwar PDP ko sabuwar APC, Ina nan daram a cikin tsohuwar APC.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tambuwal, ya sallami dukkan kwamishanoninsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Oshiomhole na ganawa da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

A halin da ake ciki, Sabon zababben shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamrad Adams Aliyu Oshiomhole na cikin ganawar sirri da masu ruwa da tsakin APC na majalisar wakilai a yanzu haka.

Oshiomhole wanda ya isa dakin ganawar, a majalisar dokoki da misalin karfe 3:00 na rana, ya samu rakiyan kakakin majalisar wakilai da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da Femi Gbajabiamila.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel