Nigerian news All categories All tags
Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

A yau, Alhamis, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da shugabannin kungiyar Kiristoci (CAN) na jihohin arewa 19 a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Wannan ba shine karo na farko da shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ta CAN ba. Saidai wannan shine karo na farko da ya gana da shugabannin kungiyar na jihohin arewa kawai.

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

Buhari da Simon Lalon na jihar Filato

Shugabannin sun ziyarci Buhari ne karkashin jagorancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

Yayin ganawar tasu, shugaba Buhari, ya bayyana takaicinsa bisa salwantar rayukan 'yan Najeriya a jihohin Zamfara, Benuwe da Filato tare da daukan alkawarin kawo karshen kashe-kashen rayuka a duk sassan Najeriya.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Yau kuma, Shugaban kasar Namibia ya ziyarci shugaba Buhari

"Na zo ofis da burin kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya kuma ba zan taba gazawa ba sai na tabbatar da tsaro a Najeriya. Ban yarda da asarar ran koda mutum daya dan Najeriya ba," a cewar shugaba Buhari.

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

Buhari da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna

Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel