Nigerian news All categories All tags
Shugaban INEC zai bayyana a gaban kotun Abuja bayan PDP ta shigar da shi kara

Shugaban INEC zai bayyana a gaban kotun Abuja bayan PDP ta shigar da shi kara

- Babban kotun tarayya dake jihar Anambra ta bukaci shugaba INEC, Mahamood Yakubu ya bayyana a gabanta don kare kansa

- Wani bangare na jam'iyyar PDP reshen Anambra ne ya shigar da INEC kara kotun inda suke ikirarin INEC taki biyaya ga umurnin kotu

- Kotun tayi watsi da bukatar hukumar INEC na yin watsi da tuhume-tuhumen da ake mata saboda rashin gamsasun dalilai

Wata babban kotun tarayya ta aike da sammaci ga hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) da shugaban ta Farfesa Mahmood Yakubu saboda wata karar saba umurnin kotu da wani bangare na jam'iyyar PDP reshen jihar Anambra ta shigar a kan hukumar.

The sun ta ruwaito cewa kotun ta bukaci shugaban INEC Mahmood Yakubu ya gurafana gaban kotun don kare kansa daga tuhumar da ake masa idan ko ba hakan ba kotu zata garkame shi saboda rashin biyaya ga umurnin ta.

Babban kotun tarayya ta aike wa shugaban INEC sammaci saboda wani laifi da ake zarginsa da aikatawa

Babban kotun tarayya ta aike wa shugaban INEC sammaci saboda wani laifi da ake zarginsa da aikatawa

DUBA WANNAN: APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

A yau Alhamis, Alkalin dake Shari'ar, Justice Stephen Pam ya yi watsi da bukatar da shugaban INEC, Yakubu ya shigar na neman kotun tayi watsi da karar da wani Ejike Oguebego da magoya bayansa a PDP suka shigar a jihar Anambra.

A yayin da ya ke yanke hukunci a kan karar da aka shigar a kan Yakubu, Pam ya yi watsi da ikirarin da Yakubu ya yi na cewa mai shigar da ya shigar da kara a wannan kotun ne don yana tunanin samun nasara duk da cewa ya shigar da irin wannan karar a wata kotun.

Pam ya kuma ce dalili na biyu da Yakubu ya bayar na cewa wanda ya shigar da karar ya kammala wa'addin mulkinsa ba kwakwaran dalili bane na hana shi shigar da kara duk da cewa INEC bata gabatar da shedan cewa mai shigar da karar ya kammala wa'addin mulkinsa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel