Nigerian news All categories All tags
An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin shelkwatar Soji da Miyetti Allah

An nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki tsakanin shelkwatar Soji da Miyetti Allah

Shelkwatar tsaro ta rundunar Sojojin Najeriya gaba daya ta musanta zargin da kungiyar Miyetti Allah ta yin a cewa wai wasu dakarun Sojoji na musamman sun kashe makiyaya guda shida da kuma shanu dari da hamsin a jihar Nassarawa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mukaddashin kaakakin shelkwatar tsaro, Birgediya Janar John Agim ne ya sanar da haka a ranar ALhamis, 5 ga watan Yuli, inda yace Dakarun Soji na musamman sun ci karo da wasu yan bindiga a Nassarawa, wanda har suka kashe Sojoji biyu da tare da jikkata da dama.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya

Da wannan ne Birgediya Agim ya bayyana maganganun da shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Nassarawa, Mohammed Hussein ya yi a matsayin karairayi, inda ya kara da cewa: “A ranar 26 ga watan Yunu da misalin karfe 6 na safe, Sojoji sun gudanar da aiki a wani sansanin makiyaya yan bindiga a kauyen Bakon Kota dake cikin karamar hukumar Keana.

“Bayan sun kammala aikin, sai yan bindigan suka sake dawowa, inda suka yi ma Sojojin zobe, suka kashe Sojoji biyu tare da jikkata wasu da dama daga ciki har da kwamandansu, wannan ne yasa aka kara shirya wasu Sojoji na musamman da suka dira kauyen, inda aka yi musayar wuta aka kashe na kashewa, tare da gano bindiga AK 47 guda daya, kananan bindigu Uku, adda da alburusai dari takwas.” Inji shi.

Daga karshe yace tunda har shugaban Miyetti Allah ya yarda cewa yayan kungiyarsu ne, bayan mu mun sani miyagun mutane, toh abin tambaya ne, amma ya sani hukumar Soji ba za ta daga ma duk wani dan bindiga kafa ba, da duk masu daukar nauyinsu.

A ranar 8 ga watan Yuni ne, shugaban hafsan hafsohin Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin ya kaddamar da rundunar Soji ta musamman,OPWS, don yakar yan bindiga a jihohin Taraba, Zamfara, Nassarawa da Benuwe, tare da tabbatar da tsaro, doka da oda.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel