Nigerian news All categories All tags
2019: Jam’iyyun siyasa 36 na shirin hadewa don kayar da Buhari – Shugaban jam’iyyar SDP

2019: Jam’iyyun siyasa 36 na shirin hadewa don kayar da Buhari – Shugaban jam’iyyar SDP

Gabanin zaben 2019 da ke shiri yanzu, wani gamayyar jam’iyyar siysa 36 a ranan Larab sun kafa kwamiti na musamman domin shirya yadda zasu zama tsintsiya madaurinki daya domin kawo karshen gwamnatin jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party SDP, Chief Olu Falae, ya bayyanawa manema labarai a birnin Abuja jiya yayinda wakilan wadannan jam’iyyu suka gana da shi a sakatariyan jam’iyyar da ke Abuja.

Cif Falae ya ce haka kan jam’iyyun ya zama wajibi ne saboda yanayin matsalolin da suka yiwa kasar yawa karkashin wannan gwamnatina rashin tsaro da tattalin arziki.

Game da cewarsa, yan Najeriya sun zama mabarata alhalin kasa na da kudi. Ya ce tun watan Fabrairu suke tattaunawa kan yadda zasu kawo cigaba kasa.

Ya kara da cewa mambobin gamayyar na tattaunawa da wasu daiddaikun kungiyoyi da mutne masu manufa iri daya domin hada kan Najeriya.

Shugaban gamayyar wanda shin shugaba jam’iyyar Justice Party, Chief Breetfort Onwubuya, sun kasance suna shirye-shirye kan yadda za su ceto kasar nan daga tabarbarewa.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa tsaffin mambobin ‘nPDP’ dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC), za su alanta fitarsu daga jam’iyyar domin sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugabannin kungiyar sun kunshi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel