Nigerian news All categories All tags
An hallaka mutane 5, biyu sun jikkata a sabuwar hari a jihar Adamawa

An hallaka mutane 5, biyu sun jikkata a sabuwar hari a jihar Adamawa

Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu a sabuwar harin da aka kai garin Mararaban Kola a karamar hukumar Guyuk a jihar Adamawa, Arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, wanda ya tabbatar da wannan labara yau Alhamis ya ce mazaje hudu da mace 1 ne aka kashe kuma an kona gidaje 7.

Abubukar ya kara da cewa wani mutum da matarsa sun samu munanan raunuka amma an kai babban asibitin Yola domin jinya.

Idanuwan shaida sun cewa wasu mahar ne suka shigo Mararaba Kola cikin daren ranan Lraba kn Babura suna harbe-harbe da kuma kon gidajen mutane.

Amma shugaban karamar hukumar, Sm Kasiwa, ya bayyanawa manema labarai ta wayan tarho cewa an tura jmi’an sojoji wajen kuma an damke mutane 2 cikin maharan.

KU KARANTA: An yi garkuwa da malamin addini

Game da kisan Plateau kuwa, mun kawo muku rahoton cewa jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democratic Party, PDP ta shiga zaman makoki na kwanaki bakwai don jimamin mutanen da aka hallaka a jihar Plateau.

Jam’iyyar ta bukaci a sassauto da tutarta a dukkanin ofisoshinta da ke fadin kasar har na tsawon kwanaki bakwai da ta ayyana na zaman makokin kisan mutane sama da 200 da akayi a jihar ta Plateau.

Kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyanawa manema labarai cewa PDP ta bukaci al’umman jihar Plateau da su yi amfani da yancinsu na yan kasa ta hanyar kai kara kotun duniya kan gazawar gwamnati wajen kawo karshen yawan kashe-kashe a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel