Nigerian news All categories All tags
Kuma dai: An yi garkuwa da malamin addini

Kuma dai: An yi garkuwa da malamin addini

An yi garkuwa da babban limamin katolikan Sacred Heart Parish, Obomkpa a jihar Delta, Reverend Andrew Anah, a karo na biyu cikin shekaru biyu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Andrew Aniamaka, ya tabbatar da wannan labari ga manema labarai da safiyar yau Alhamis, 5 ga watan Yuli 2018.

An yi garkuwa da wannan limamin a shekarar 2017 amma aka sake shi bayan biyan fansa ga masu garkuwa da mutanen.

Duk da cewa har yazu babu labarin yadda sukayi garkuwa da shi, tashar Channels TV ta tattara cewa wasu mazauna garin na hada baki da masu garkuwa da mutanen wajen aikata wadannan ayyukan.

KU KARANTA: Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya shiga ganawar sirri da wasu gwamnonin APC

Mazauna sunce garin Obomkpa/Ukwu-Nzu da Aniocha ya lalace da garkuwa da mutane yanzu. Kwanakin nan an yi garkuwa da shugaban wani kamfanin gine-gine da kuma shugaban kwamitin sarakunan gargajiyan garin, Mr Obi Sunday Olisenweokwu.

Amma hukumar yan sanda suna bada tabbacin cewa za su yi iyakan kokarin wajen ceto wadannan mutanen.

Kuma dai: An yi garkuwa da malamin addini

Kuma dai: An yi garkuwa da malamin addini

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) ya bayyana tsaro a Najeriya a matsayin abin tsoro bayan masu garkuwa sun sace mahaifinsa a karo na biyu.

A ranar 26 ga watan Yuni ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace mahaifin Obi tare da direbansa bayan sun nuna masu bindiga.

An sanar da Obi batun sace mahaifin nasa sa’o’I hudu kafin wasan da Najeriya ta buga da kasar Argentina. Sannan an sako shi a jiya, Litinin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel