Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Adamu Ciroma rasuwa yana da shekara 84

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Adamu Ciroma rasuwa yana da shekara 84

Rahotanni dake isowa gare mu a yanzu ya nuna cewa Allah ya yi wa Malam Adamu Ciroma rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a asibitin Turkish dake babban birnin tarayya Abuja a yau Alhamis, 5 ga watan Yuli.

An haifi Malam Adamu a ranar 20 ga watan Nuwamba, 1934 a garin Potiskum dake jihar Yobe, inda ya rasu yana da shekaru 84.

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Adamu Ciroma rasuwa yana da shekara 84

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Adamu Ciroma rasuwa yana da shekara 84

Marigayin ya kasance babban jigo a siyasar Najeriya, kafin rasuwar sa ya rike mukamin Gwamnan babban bankin Najeriya, sannan kuma ya rike mukamin ministan kudi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa na bincike akan kisan jami’an yan sanda 7 da aka yi a Abuja

Nan da lokaci kadan za a sanar da lokaci da wurin da za a gudanar da jana'izarsa. Allah ya gafarta masa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel