Nigerian news All categories All tags
Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA

Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA

Ministan wasanni na Najeriya, Solomon Dalung, ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), data kai kara gaban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA), akan yanda aka yiwa Najeriya rashin adalci a gasar cin kofin duniya da aka gabatar a kasar Rasha

Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA

Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA

Ministan wasanni na Najeriya, Solomon Dalung, ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), data kai kara gaban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA), akan yanda aka yiwa Najeriya rashin adalci a gasar cin kofin duniya da aka gabatar a kasar Rasha.

DUBA WANNAN: An kashe sojoji 2, sannan an jiwa kwamanda da wasu sojoji 5 ciwo

Mista Dalung yace rashin adalacin da aka yiwa Najeriya ya fito daga bangaren alkalan wasane, kuma hakan shine musabbabin rashin samun nasarar Najeriya a wasan da suka buga da kasashen Argentina da Croatia.

A wannan shekarar ne dai aka fara amfani da na'ura mai daukar bidiyo domin taimakawa alkalin wasa wurin yanke hukunci akan abubuwan da suka faru a filin wasa wanda hankalin sa baya kai.

'Yan Najeriya basu ji dadin abinda alkalin wasan Najeriya da Argentina yayi ba, na kin bayar da Fenariti duk kuwa da cewa bidiyo ya nuna yanda kwallon ta taba hannun dan wasan Argentina din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel