Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin APC sun yi shiru bayan ganawa da Buhari

Gwamnonin APC sun yi shiru bayan ganawa da Buhari

A ranar yau Alhamis, 5 ga watan Yuli ne gwamnonin APC uku suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin sirri.

Sai dai sun ki bayyana musabbabin ganawar tasu da shugaban kasa ga manema labarai.

An gunadar da ganawar ne a cikin ofishin shugaban kasa dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Gwamnonin da suka halarci wannan ganawa sune Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, Abubakar Badaru na jihar Jigawa da kuma Abubakar Bagudu na jihar Kebbi.

Gwamnonin APC sun yi shiru bayan ganawa da Buhari

Gwamnonin APC sun yi shiru bayan ganawa da Buhari

Shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Abba Kyari ne ya jagorance su zuwa ofishin shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa na bincike akan kisan jami’an yan sanda 7 da aka yi a Abuja

Gwamnonin sun ki cewa uffan lokacin da manema labarai na fadar shugaban kasa suka tunkare su.

Da manema labarai suka matsa don son jin ko ganawar na da alaka da rikicin jam’iyyar, Yari ya amsa masu da cewa: “Ganawa ce ta sa kai baida alaka da APC."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel