Nigerian news All categories All tags
Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar gidan gwamnatin jihar Imo saboda kasa biyan bashi

Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar gidan gwamnatin jihar Imo saboda kasa biyan bashi

Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar Gidan Gwamnatin Jihar Imo, saboda kasa biyan bashin da take bi na wuta har naira miliyan 200 da ta sha.

Sannan kuma kamfanin ya yanke wutar Sakateriyar Gwamnatin Jihar Imo duk saboda taurin bashi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa takaicin hakan ne ya sanya ofishinn kula da tsarin gine-gine na jihar ya yi wa ofishin wutar jan fentin da ke nuna za a ruguje shi gaba daya.

Kakakin Hukumar, Emeka Ezeh ya tabbatar da faruwar wannan lamari na yanke wutar gidan gwamnatin, sai dai gwamnatin ta kai gwauro ta kai mari wajen kokarin ganin an biya bashin wutar.

Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar gidan gwamnatin jihar Imo saboda kasa biyan bashi

Kamfanin bada wutar lantarki ya yanke wutar gidan gwamnatin jihar Imo saboda kasa biyan bashi

Ya kuma ce su na sane da cewa an zana wa ofishin su jan fenti an kuma rubuta umarnin za a ruguje shi cikin kwanaki bakwai.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Bauchi sun sanya shugaba Buhari a gaba kan Dogara

Sannan ya kara tabbatar da miliyoyin kudaden da suke bin Sakateriyar Gwamnatin Jiha da kuma ofishin gwamna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel