Nigerian news All categories All tags
Tazarcen gwamnan Kaduna na tanga-tangal: Tsohon daraktan yakin neman zaben Nasir El-Rufa'i ya fice daga Jamiyyar APC

Tazarcen gwamnan Kaduna na tanga-tangal: Tsohon daraktan yakin neman zaben Nasir El-Rufa'i ya fice daga Jamiyyar APC

- Jam'iyyar APC na fuskantar zaizayar kasa gabannin zaben 2019

- Wannan zaizaiya dai ta shafi jihar Kaduna, inda tsohon daraktan kamfe na El-Rufa'i ya sauya sheka

- Wani sanata ma kuma ana rade-radin cewa shi ma zai kama hanyar fita daga jam'iyyar

Ja’afaru Ibrahim wanda shi ne tsohon daraktan yakin neman zaben gwamnan jihar Kaduna a zaben Shekarar 2015 ya dangwarar da shahadar kasancewarsa mamba a Jamiyyar APC, cikin wata takarda da ya aikewa shugaban mazabarsa ta kwarbai da ke birnin Zaria.

Tazarcen gwamnan Kaduna na tanga-tangal: Tsohon daraktan yakin neman zaben Nasir El-Rufa'i ya fice daga Jamiyyar APC

Tazarcen gwamnan Kaduna na tanga-tangal: Tsohon daraktan yakin neman zaben Nasir El-Rufa'i ya fice daga Jamiyyar APC

Da ya ke bayyana dalilansa na ficewa daga jamiyyar ta APC ya ce, jamiyyar ta zama wani jirgin ruwa da ruwan ya ke kokarin cinye shi, ya kuma bayyana takaicinsa game da yadda gwamnan jihar ta Kaduna, Malam Nasiru El-rufa'i ya yi watsi da manufofin jamiyyar da aka kafa ta akai.

KU KARANTA: Yanzu- yanzu: Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya shiga ganawar sirri da wasu gwamnonin APC

Ya kara da cewa gwamnatin Nasiru El-rufa'i ta kasa magance matsalar da ta da mu al'ummar jihar Kaduna, musamman rashin samar da aikin yi, da aiyukan more rayuwa.

Tun da farko dai jamiyyar APC reshen jihar Kaduna ta fuskanci fitar manyan yayanta wadanda su ka hadar da Yaro Makama Rigachiku, Isa Ashiru, Jagaba Adams Jagaba da kuma Hakeem Baba Ahmed, wanda ya kasance shi ne shugaban ma'aikata na shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel