Nigerian news All categories All tags
2019: Dalilin da ya sa na shiga jam’iyyar PDP – Ahmed Buhari

2019: Dalilin da ya sa na shiga jam’iyyar PDP – Ahmed Buhari

Daya daga cikin matasan Najeriya day a nuna ra’ayin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019, Ahmed Buhari, ya sanar da cewa ya shiga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Matashin mai shekaru 40 a duniya ya bayyana hakan a karshen mako a Abuja inda matasa da sama da 4,000 suka yo masa rakiya.

A wajen taron kaddamar da kudirin nasa, ya sanar da ra’ayinsa na son takarar a karkashin jam’iyyar PDP, wato babban jam’iyyar adawar kasar.

2019: Dalilin da ya sa na shiga jam’iyyar PDP – Ahmed Buhari

2019: Dalilin da ya sa na shiga jam’iyyar PDP – Ahmed Buhari

Da yake bayyana dalilin sa na shiga jam’iyyar PDP a shafinsa na twitter @OfficialAhmedB ya ce zai yi wuya ya kayar da abokin takarar sa a karkashin jam’iyyar da bata shahara ba.

KU KARANTA KUMA: Sabbin shugabannin gyararriyar APC na kasa da Jihohi (jerin sunaye)

Buhari wanda ya kasance shugaban Skylar Inc., wani kamfani dake Lagas, ya bukaci mambobi da magoya bayan PDP da su ajiye matsayi domin hada kai wajen kayar da jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel