Nigerian news All categories All tags
APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta bukaci ya watsi da dan takarar jam'iyyarsa ta PDP, Kolapo Oluwola ya marawa Kayode Fayemi na APC baya a zaben gwamna mai zuwa a jihar.

Fayose wanda 'dan jam'iyyar PDP ne na keke-da-keke ne ya yi wannan magana ne a daren Talata yayin hira da akayi dashi a wata gidan talabijin da rediyo na jihar Ekiti.

Sai dai jam'iyyar APC ta musanta batun na gwamnan inda ta ce kawai yana neman ya juyar da hankulan masu zabe ne kana ya bawa mutane abin magana.

APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama shugaban 'yan fashin da yaransa suka dakatar dashi a Kano

"Mambobin jam'iyyar APC sun same ni inda suk bukaci in juya wa Olusola baya domin Kayode Fayemi ya yi nasara," a cewar gwamnan.

"Sun bani misalai da wasu shugabani da suka sayar da tikitin nasu kuma suka tambaye ni ko nima ina sha'awan yin hakan.

"Amma sai na fada musu gar-da-gar ni ba zanyi hakan ba. Idan wasu na hakan ni bazanyi ba saboda ni mutum ne mai nagarta. Na dauki alkawarin kayar da Fayemi da APC. Bayan Ekiti liyafa zata cigaba a Abuja," inji shi.

Fayose ya cigaba da cewa sun fada masa cewa ya fiye taurin kai amma ya fada musu taurin kansa saboda shi mutum ne mai tsari kuma mutane Ekiti sun san matsayarsa kuma ba zai ci amanansu ba saboda suna kaunarsa da jam'iyyarsa.

Sai dai jam'iyyar APC ta karyata zancen na Fayose inda tace wannan kawai wata sabuwar tabatgaza ne da ya saba yi.

Jam'in yadda labarai na jam'iyyar, Taiwo Olatunbosun yace babu alamar gaskiya cikin zancen na Fayose inda yace mutanen EKiti basu yin Fayose da PDP saboda basu kaunar abinda kowa ke kyamata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel