Nigerian news All categories All tags
Allah da lokaci ne kadai za su iya kawo karshen APC amma ba sabuwar PDP ba - Ndume

Allah da lokaci ne kadai za su iya kawo karshen APC amma ba sabuwar PDP ba - Ndume

Sanata mai wakiltan kudancin Borno, Ali Ndume, ya bayyana cewa duk barazanar da yan kungiyar sabuwar PDP ke yin a barin jam’iyyar APC ba zai taba kawo karshen jam’iyyar ba saboda Allah da lokaci ne kadai zasu yi nuni ga hakan.

Sanatan yayin da yake Magana da manema labarai a babban sakatariyar APC na kasa a ranar Laraba, ya ce siyasa duk ra’ayi ne sannan kuma cewa babu laifi dan kungiyar hasalallu sun bayyana zuciyarsu.

Ya kuma bayyana cewa barazanar sauya sheka da yan sabuwar PDP ke yi ba zai hana APC yin nasara a zaben 2019 ba.

Allah da lokaci ne kadai za su iya kawo karshen APC amma ba sabuwar PDP ba - Ndume

Allah da lokaci ne kadai za su iya kawo karshen APC amma ba sabuwar PDP ba - Ndume

Mista Ndume ya bayyana hakan ne a yayinda ya je taya sabon shugaban jam’iyyar APC murna a Satariya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana jam’iyyar APC mai mulki a matsayin mai nuna alamu na kiyayya da hasada.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Lamido, wanda yayi Magana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a gangaminsa na jihohi don neman goyon baya ga kudirinsa na neman kujerar shugabancin kasa, ya ce APC na bata duk wani a kasar idan dai har bai kasance daya daga cikin yan sansaninta ba.

Ya ce jam’iyyar PDP ce ta mulki kasar na tsawon shekara 16 wacce ita ce ta raini mafi akasarin yan APC harma wadanda ke da kusanci da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel