Nigerian news All categories All tags
Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Sabon zababben shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya roki fusatattun ‘yan jam’iyya da suka kafa sabuwar APC mai suna gyararriyar APC wato ‘reformed APC’ da su mai da wukar su, sannan su dan bashi lokaci domin shawo kan matsalolin da ke cunkushe a jam’iyyar.

Oshiomhole ya ce: “Ina rokon ku da kuyi hakuri.”

A cewarsa yana so ya basu tabbacin cewa a matsayin sa na sabon shugaban jam’iyyar yanzu, idan aka tunashe shi zai waiwayo ya gyara dukkanin kura-kuran da ake zargin jam'iyyar da tafkawa.

Ya kara da cewa yanzu ne aka zabe su kuma da shi da sauran sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar za su mai da hankali wajen ganin sun gyara kuskuran da aka yi a baya.

Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

“Ni dinnan zan yi aiki da duk wani dan jam’iyyar mu sannan kuma zan hado kan kowa kuma za ayi tafiya ne tare babu wariya ko kumu nuna bambamci ga wasu. Ina bukatan ku dan bani lokaci domin ni zan bi diddigin yadda komai yake ne tun a farko in kuma gyara.” Inji Oshiomhole

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa manyan sanatoci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All progressives Congress (APC) sun yi ganawa mai muhimmancin da kwamitin aikin jam’iyyar na kasa. Sun gana ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel