Nigerian news All categories All tags
APC na nuna kwatancin kiyayya – Dan takarar shugabancin kasa a PDP

APC na nuna kwatancin kiyayya – Dan takarar shugabancin kasa a PDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana jam’iyyar APC mai mulki a matsayin mai nuna alamu na kiyayya da hasada.

Lamido, wanda yayi Magana a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a gangaminsa na jihohi don neman goyon baya ga kudirinsa na neman kujerar shugabancin kasa, ya ce APC na bata duk wani a kasar idan dai har bai kasance daya daga cikin yan sansaninta ba.

Ya ce jam’iyyar PDP ce ta mulki kasar na tsawon shekara 16 wacce ita ce ta raini mafi akasarin yan APC harma wadanda ke da kusanci da shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

APC na nuna kwatancin kiyayya – Dan takarar shugabancin kasa a PDP

APC na nuna kwatancin kiyayya – Dan takarar shugabancin kasa a PDP

“Toh ya batun wadanda suka kasance tsatson PDP dake bangaren siyasar shugaban kasar, me ya sa ba’a sanya masu sunan barayi ba? Suna kiran mu da yayanmu barayi. Shin suna nufin nasu yayan waliyai ne?” Ya tambaya.

KU KARANTA KUMA: Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa manyan sanatoci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All progressives Congress (APC) sun yi ganawa mai muhimmancin da kwamitin aikin jam’iyyar na kasa.

Sun gana ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli domin nemo maslaha ga rikicin jam'iyyar wanda ya sa mutane ke ficewa daga jam'iyyar daya bayan daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel