Nigerian news All categories All tags
Atiku ya bukaci 'yan majalisa dasu kara taso da maganar 'yan sandan jiha

Atiku ya bukaci 'yan majalisa dasu kara taso da maganar 'yan sandan jiha

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjiinawa majalisar dattawa akan yanke shawarar kara duba ga kudurin kaddamar da 'yan sandan jiha a cikin kundin tsarin mulkin kasar domin kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar nan

Atiku ya bukaci 'yan majalisa dasu kara taso da maganar 'yan sandan jiha

Atiku ya bukaci 'yan majalisa dasu kara taso da maganar 'yan sandan jiha

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjiinawa majalisar dattawa akan yanke shawarar kara duba ga kudurin kaddamar da 'yan sandan jiha a cikin kundin tsarin mulkin kasar domin kawo karshen matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

A jawabin da yayi a ofishin yada labaran shi a ranar Alhamis a Abuja, yace yan majalisar sun nuna kwarin guiwa gurin hana yunkurin kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

Ya tuna da zubar da jinin mutanen jihohin Zamfara, Binuwai, Filato, Taraba, Adamawa da Kaduna da kuma kisan yan sanda 7 dake kan aikin su a Abuja.

Atiku yace ganin yanda al'ummar kasar basu da tsimi balle dabara yasa samar da yan sandan jiha da kuma kauyuka ya rataya a wuyan yan majalisar domin kawo karshen hare haren da suka ki karewa.

"Kowanne matsala tana da abinda ya dace ayi domin magance ta, kuma ina tare da yan majalisar dari bisa dari a yunkurin su na tabbatar da gwamnatin jihohin domin su samar da tsaro ga al'ummar kasar nan," inji Atiku.

A karshe ya mika sakon ta'aziyyar shi ga iyalai da yan uwan yan sandan 7 da aka kashe a Abuja ranar Talatar nan.

"Dole ne Najeriya ta fito ta nunawa jama'a a fili cewar rayuwar jami'an tsaron mu nada amfani, mutuwar daya a cikin su asara ce ga kowa a kasar nan."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel