Nigerian news All categories All tags
Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff

Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bukaci kabilar Igbo dasu goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar a shekarar 2023

Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff

Dole a baiwa kabilar Igbo damar shugabancin kasar nan - Sheriff

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bukaci kabilar Igbo dasu goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar a shekarar 2023.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

Tsohon gwamnan yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake magana da manema labarai a garin Umuahia babban birnin jihar Abia, a lokacin da ya kai ziyara wurin shugabannin jam'iyyar APC na jihar.

"Bisa dukkan alamu da kuma abinda idona yake nuna, jam'iyyar APC ce kadai jam'iyyar da take da karfin da zata iya lashe zaben jihar Abia a shekarar 2019, sannan kuma ina matukar bawa mutanen wannan yanki shawara dasu goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya, domin hakan shine zai basu damar samun kujerar shugabancin kasar nan a shekarar 2023.

"Siyasar kasar nan daban ce da sauran kasashe, kabilar Igbo ba zai yiwu ku zauna kawai kuna tunanin cewa za'a dauki kujerar shugabancin kasar nan a danka muku ba; saboda haka indai kun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari, na tabbata zaku samu kujerar shugabancin kasar nan a shekarar 2023," Inji Sheriff.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel