Nigerian news All categories All tags
Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

A jiya ne majalisar wakilai suka yi taro akan, matsalar rashin aikin yi, sannan kuma sun tattauna akan tsarin da za'a fito dashi na rage shekaru wurin daukar ma'aikata a dukkan ma'aikatu da hukumomin fadin kasar nan

Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

Majalisar wakilai ta cire wata doka da take ciwa masu neman aiki tuwo a kwarya a kasar nan

A jiya ne majalisar wakilai suka yi taro akan, matsalar rashin aikin yi, sannan kuma sun tattauna akan tsarin da za'a fito dashi na rage shekaru wurin daukar ma'aikata a dukkan ma'aikatu da hukumomin fadin kasar nan.

Majalisar ta bukaci dukkanin hukumomin gwamnati, da ma'aikatu dasu fara daukar ma'aikata daga kan masu shekaru 30 zuwa 40.

DUBA WANNAN: An baiwa ministocin Birtaniya wasiyyar yanda zasu yi jana'izar Sarauniyar Ingila

Kawo tsarin ya biyo bayan korafi da wani dan majalisa ya kai Babajimi Benson (APC, Lagos), wanda yayi magana akan cewar kowacce ma'aikata idan zata dauki ma'aikata suna daukan wadanda basu kai shekaru 30 ba ne a duniya. Inda dan majalisar ya kara da cewa saka doka akan shekaru ya sabawa dokar kasar nan, sannan kuma tauye hakkin al'umma ne ace dole sai wadanda suke kasa da shekaru 30 za'a dauka aiki.

Ya ce, "In dai haka za'a cigaba to duk mutanen da suka yi bautar kasa, wadanda suke da shekaru 30 bai yi musu amfani ba kenan tunda babu wanda zai dauke su aiki, idan ma an dauke su to dole sai dai suyi karyar rage shekarun su."

Benson ya kara da cewa, da a saka doka akan shekaru wurin daukar aiki, da doka aka saka akan cancantar mutum.

A karshe dai bayan doguwar muhawara da majalisar tayi, sun yanke hukuncin kara shekarun daukar ma'aikatan a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel