Nigerian news All categories All tags
Zan cefanar da duk wani kadarar da muka kwato daga hannun barayin gwamnati – Buhari

Zan cefanar da duk wani kadarar da muka kwato daga hannun barayin gwamnati – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Duniya na kallo kuma zata cigaba da lura ko gwamnatin da zata gaji gwamnatinsa za ta mayar da kadarorin da suka kwato daga hannayen barayin gwamnati a garesu.

Jaridar Punch ta ruwaito Buhari na fadin an taba yi masa haka a shekarar 1983, inda yace sun kwato kadarori da dama daga hannayen barayin gwamnati, amma bayan da wata gwamnatin ta hambarar da gwamnatinsa, sai ta mayar da kadarorin ga barayin.

KU KARANTA: Buhari ya shirya kashe naira Tiriliyan 2.1 don kammala aikin wutar mambila

Zan cefanar da duk wani kadarar da muka kwato daga hannun barayin gwamnati – Buhari

Buhari da Geinob

Da wannan ne Buhari yace an sha shi ya warke, don haka zai sayar da duk kadarorin ne tare da sanya kudin cikin asusun gwamnati don amfanin yan Najeriya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa.

Buharin ya bayyana haka ne a fadar gwamnati dake Abuja, a yayin ganawa da manema labaru tare da shugaban kasar Namibia, Hage Geingob da ya kawo ziyara Najeriya, yace: “Muna bin mutane muna kwace kadarorin da suka mallaka ta hanyar sata, muna bibiyan asusun bankunansu da na kamfanoninsu.

“Kuma ko a baya, bayan da aka yi min juyin mulki aka daureni, gwamnati ta mayar da barayin gwamnari kadarorin da muka kwato daga hannayensu, don haka a yanzu zamu sayar dasu kuma mun zubasu a baitula mali, sai muga wanda zai debi kudin ya mayar musu.

“Muna samun nasara a yakin da muke yi da rashawa, amma lamarin da wahala musamman a dimukradiyya irin tamu, amma tuda dai kasashen waje sun bamu hadin kai, zamu cigaba da siyar da duk wata kadara da muka kwato don amfanin talaka.” Inji shi.

A nasawa jawabin, shugaban Namibia, Geinob ya gode ma Najeriya da tallafin fa take baiwa kasarsa da ma’aikatan sa kai, inda yace yazo ya halarci jana’izar tsohon shugaban hukumar dake aikawa da ma’aikatan, Farfesa Adebayo Adedeji da za’a yi a ranar Asabar.

Sa’annan yace shuwagabannin kasashen Afirka suna koyi yaki da rashawa daga Buhari, “don nima a kasata na kaddamar da yaki da rashawa da kuma yaki da talauci.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel