Nigerian news All categories All tags
Tsaro: Atiku na goyon bayan majalisa kan batun 'yansandan jihohi

Tsaro: Atiku na goyon bayan majalisa kan batun 'yansandan jihohi

- Wasu na ganin idan jihohi na da 'yansandansu za'a sami tsaro

- Wasu kuma na ganin gwamnoni zasu yi karfi sosai

- Atiku na bayan majalisa kan batun a baiwa jihohi dama a doka

Tsaro: Atiku na goyon bayan majalisa kan batun 'yansandan jihohi

Tsaro: Atiku na goyon bayan majalisa kan batun 'yansandan jihohi

Matsalar tsaro ta addabi jihohin kasar nan, inda ko wanne yanki yake fama da nasa, daga rikicin manoma-makiyaya, sai na kabilanci, sai na addinanci, da ma na siyasa, sai kuma na 'yan daba, da ma na 'yan fashi da masu garkuwa da mutane.

A kuma bangare daya, akwai matsalar ta'addanci, inda Boko Haram ke kan ganiyar durkusar da kasar baki daya.

Kokarin dawo da zaman lafiya ya sanya wasu ke ganin tunda gwamnatin Najeriya ta kasa, a baiwa jihohi damar su tsare jama'arsu da kansu.

DUBA WANNAN: An kashe dan AlBaghdadi a Siriya

Bayan da shuwagabannin majalisa suka nuna suna goyon bayan hakan, yanzu shima tsohon mataimakin shugaba Obasanjo, Atiku Abubakar, yace, ya dawo daga rakiyar gwamnatin tarayya, domin ta gaza tsare jama'a, don haka, a baiwa gwamnoni damar daukan jami'an tsaron jama'arsu a hukumance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel