Nigerian news All categories All tags
Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar (hotuna)

Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar (hotuna)

Manyan sanatoci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All progressives Congress (APC) sun yi ganawa mai muhimmancin da kwamitin aikin jam’iyyar na kasa.

Sun gana ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli duk da cewar ba’a bayyanawa jama’a cikakken bayanin ganawar ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An nada na kusa da Buhari a matsayin shugaban sabuwar APC

Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci (hotuna)

Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci

Manyan mutanen da suka halarci ganawar sun hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Gannawar na zuwa ne a daidai lokacin da jita-jita ya yawaita na cewa Saraki na shirin barin jam’iyyar tare da sauran mambobin sabuwar PDP.

Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci (hotuna)

Sanatocin APC sun yi ganawa mai muhimmanci

A halin da ake ciki, Wata sabuwar kungiya ta balle daga jam’iyyar All progressives Congress (APC) ta kuma sanya wa kanta suna a matsayin sabuwar APC wato Reformed All Progressives Congress (RAPC).

A cewar Sahara Reporters, sabuwar APC daya take da sabuwar PDP wacce ta hade da APC a lokacin zaben 2015.

An nada Buba Galadima wanda ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar Congress for Progressive Change kuma makusanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban sabuwar kungiyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel