Nigerian news All categories All tags
Babbar Magana: An kama wani gwamna mai ci saboda cin hanci da satar kudin jama’a

Babbar Magana: An kama wani gwamna mai ci saboda cin hanci da satar kudin jama’a

Hukumar da’a da yaki da cin hanci ta kasar Kenya (EACC) ta tabbatar da kama wani gwamna mai ci kasar bisa tuhumarsa da cin hanci da satar kudin jama’a.

Mai gabatar da kara na hukumar EACC a kasar Kenya, Noordin Haji, ya bayyana cewar sun gurfanar da gwamnan, Sospeter Ojaamong, bayan samun sad a laifin hada baki domin satar kudi da cin amanar jama’a.

Babbar Magana: An kama wani gwamna mai ci saboda cin hanci da satar kudin jama’a

Gwamna Sospeter Ojaamong

Haji ya kara da cewar shiadar da hukumar EACC ta gabatar gaban kotu ta isa a yankewa gwamna Ojaamong hukunci. Ya sanar da cewar, gwamnan da wasu mutane 9 sun saci miliyoyin kudin jama’a tare da bayyana cewar, “sabanin ragowar tuhumar cin hanci da muke yiwa masu rike da mukaman gwamnati, wannan karon ba zargi muke yi ba, muna da shaida a hannu musamman wasu aiyuka da aka fitar da kudinsu ba tare da an dasa koda tubali ba.”

DUBA WANNAN: Kudin makamai: EFCC ta kwace Otal din N1bn da gidan N500m daga hannun wasu na kusa da Jonathan da Dasuki

Gwamnatin Uhuru Kenyatta, shugaban Kenya, da aka sake zaba a karo na biyu a shekarar 2017, ta ci al-washin sabunta yaki da cin hanci a kasar. A watanni biyu da suka wuce, gwamnatin ta gurfanar da ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati da dama bisa zarginsu da hannu a badakala da almundahana daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel