Nigerian news All categories All tags
Yanzu Yanzu: An nada na kusa da Buhari a matsayin shugaban sabuwar APC

Yanzu Yanzu: An nada na kusa da Buhari a matsayin shugaban sabuwar APC

Wata sabuwar kungiya ta balle daga jam’iyyar All progressives Congress (APC) ta kuma sanya wa kanta suna a matsayin sabuwar APC wato Reformed All Progressives Congress (RAPC).

A cewar Sahara Reporters, sabuwar APC daya take da sabuwar PDP wacce ta hade da APC a lokacin zaben 2015.

An nada Buba Galadima wanda ya kasance tsohon sakataren jam’iyyar Congress for Progressive Change kuma makusanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban sabuwar kungiyar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Galadima ya zargi APC da kokarin hada sabuwar PDP aiwatar da lamuran jam’iyyar.

Yanzu Yanzu: An nada na kusa da Buhari a matsayin shugaban sabuwar APC

Yanzu Yanzu: An nada na kusa da Buhari a matsayin shugaban sabuwar APC

Ya ce daga yanzu sunan jam’iyyar RAPC sannan kuma cewa an nada dukkanin shugabanni yankuna.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso na iya barin APC a yau din nan

Kungiyar tayi ikirarin cewa APC ta yaudari miliyoyin yan Najeriya da suka zabe ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel