Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Gabanin sauya sheka zuwa PDP, Tambuwal ya sallami dukkan kwamishanoninsa

Yanzu-yanzu: Gabanin sauya sheka zuwa PDP, Tambuwal ya sallami dukkan kwamishanoninsa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya salami dukkan kwamishanoninsa yanzu-yanzun nan.

Rahotannin na nuna cewa yana cikin mambobin ‘sabuwar PDP’ da canza sune zuwa ‘sabuwar APC’ da suke shirin komawa tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP a yau.

Mambobin kungiyar wanda ya kunshi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da sauransu.

Kwanan nan, gwamna Tambuwal ya fadawa kwamishanoninsa cewa yana shirin barin jam’iyyar APC, amma majiya ya bayyana cewa kwamishanonin bsu ji dadin wannan abu ba.

KU KARANTA: Har yanzu bamu san yawan man feturin da ake sha a Najeriya ba - NNPC

Majiya mai kwari ya bayyana da jaridar Daily Nigerian cewa: “Kwamishanoni kalilan suka goyi bayan maganar. Saboda haka ba zai kyautata ya sauya sheka zuwa PDP ba tare da kwanishanoninsa ba,”.

Yayinda daukan wannan mataki, Tambuwal ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, ranan Talata a garin Minna domin neman shawara inda suka tattauna har na tsawon sa’o’I biyu.

Amma mai magana da yawunsa, Abu Shekara, yace gwamnan ya yi hakan ne domin sauyi ne kawai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel