Nigerian news All categories All tags
APC Kaduna: El-Rufai ya mayar da jam’iyyar kamar nasa – Shehu Sani

APC Kaduna: El-Rufai ya mayar da jam’iyyar kamar nasa – Shehu Sani

Sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya mayar da jam’iyyar APC kamar kamfaninsa.

Sani yayi Magana a ranar Talata a wajen wani taron gabatar da wata takarda mai suna: “Balarabe Musa: Muryar jama’a,” taron da ya samu halartan Oshiomhole.

“Misali ace, idan daga jihar Lagas nake, zan kasance a APC har abada. Idan daga Borno ne, zan kasance a APC har abada sannan idan a sauran jihohi kamar Edo nake zan kasance a APC. Amma a lamarin Kaduna gwamnan ya mayar da jam’iyyar kamar kamfaninsa.

APC Kaduna: El-Rufai ya mayar da jam’iyyar kamar nasa – Shehu Sani

APC Kaduna: El-Rufai ya mayar da jam’iyyar kamar nasa – Shehu Sani

“Babu majalisa. Kawai yana fitar da mutane da ra’ayinsu ya sha bambam da nashi sannan yana huknta mutane. Yana ruwan bala’i ga yan jam’iyya. Gwamnan ya lalata tushen jam’iyyar a jihar.”

KU KARANTA KUMA: An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

Ahalin yanzu, Sanata Shehu Sani yace dole su bar Jam’iyyar domin babu wani dalilin cigaban su na zama a APC kamar wasu Bayin ‘Yan siyasa.

Ya ce Adams Oshiomole ya zo Jam’iyyar a makare domin babu abin da zai canza a Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel