Nigerian news All categories All tags
Kwankwaso na iya barin APC a yau din nan

Kwankwaso na iya barin APC a yau din nan

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso na iya barin jamiyyar All Progressives Congress (APC) a yau din nan.

Hadimansa da dama da magoya bayansa sun je shafukan zumunta a safiyar yau inda suke bayyana cewa Kwankwaso zai bayyana sauya shekarsa a yammacin yau.

Sun bayyana cewa abun da sanatan zai yi a yau da maraice zai chanja daukacin siyasar Najeriya har abada.

Kwankwaso na iya barin APC a yau din nan

Kwankwaso na iya barin APC a yau din nan

Hadimarsa, Binta Spikin wacce ta je shafin Fabook, ta takaita da cewa Kwankwaso ya bar APC amma Kalmar da tayi amfani da shi ya nuna karara cewa an daina wasar buya tsakanin bera da mage.

A halin yanzu, Labarin da shigowa ba da dadewan nan ban a nuna cewa tsaffin mambobin ‘nPDP’ dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC), za su alanta fitarsu daga jam’iyyar domin sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

Shugabannin kungiyar sun kunshi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahoto daga jihar Premium Times ya bayyana cewa wannan sabuwar kungiya za su shirya hira da manema labarai da yammacin yau Laraba domin alanta niyyarsu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel