Nigerian news All categories All tags
Ka cecemu ka mayar da mu wata jam’iyya – Sanatocin APC na Kwara ga Saraki

Ka cecemu ka mayar da mu wata jam’iyya – Sanatocin APC na Kwara ga Saraki

Gabannin zaben 2019, sanatocin APC dake jagoranci mazabu uku na jihar Kwara sun bukaci shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da ya ja su zuwa wata jam’iyya inda zasu cimma manufar yan Kwara.

Sun bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yali.

Sanatocin APC din guda uku sun hada da Alhaji Jimoh Balogun (Kwara ta kudu), Alhaji Jimoh Adesina (Kwara ta tsakiya) da kuma Alhaji Isiaka Oniwa (Kwara ta Arewa).

Ka cecemu ka mayar da mu wata jam’iyya – Sanatocin APC na Kwara ga Saraki

Ka cecemu ka mayar da mu wata jam’iyya – Sanatocin APC na Kwara ga Saraki

Sanatocin sun yi wannan kiran ne bisa ga cewa APC da suka sha wahala ba dare ba rana don rayata a 2015 ta gaza cika masu kudirinsu.

KU KARANTA KUMA: Kama ka da hukumar DSS suka yi sadaukarwa ne ga dimokradiyyar Najeriya – Saraki ga Sanata Abaribe

A halin da ake ciki labarin dake zuwa mana ya nuna cewa tsaffin mambobin ‘nPDP’ dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC), za su alanta fitarsu daga jam’iyyar domin sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugabannin kungiyar sun kunshi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel