Nigerian news All categories All tags
Sanatan da kotu ta tsige ya halarci zaman majalisa

Sanatan da kotu ta tsige ya halarci zaman majalisa

Duk da cewar babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ta soke zaben Sanata Atai Aidoko na jihar Kogi ta Gabas, sanatan ya halarci zaman majalisa a ranar Talata, 3 ga watan Yuli.

A ranar 13 ga watan Yuni ne kotun ta dakatar da shi sannan kuma ta yi umurni kan cewa kujerarsa ta zauna ba kowa har zai gabatar da zabe.

Babban mai Shari’a Gabriel Kolawole ne ya dakatar da sanatan wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP, bayan da ya tabbatar da rashin ingancin zaben fidda-gwanin da aka gudanar a watan Disamba, 2014.

Sanatan da kotu ta tsige ya halarci zaman majalisa

Sanatan da kotu ta tsige ya halarci zaman majalisa

Kolawole ya ce ba Aidoko ba ne ya cancanci zama dan takarar jam’iyyar PDP ba.

KU KARANTA KUMA: Kama ka da hukumar DSS suka yi sadaukarwa ne ga dimokradiyyar Najeriya – Saraki ga Sanata Abaribe

Yayin da PDP ta bayyana nasarar Aidoko, sai abokin karawar sa, Isaac Alfa ya kai kara inda ya nuna rashin cancantar Aido.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa A ranar Laraba, 4 ga watan Yuli, mambobin majalisar wakilai sun yanke shawarar kafa wata kwamiti don bincikar kudin da Janar Sani Abacha ya sata ya boye a waje wanda aka dawo da su tun daga 1998 zuwa yanzu.

A karshen binciken ana sa ran kwamitin zata tono duk wasu kudade da aka gano da kuma yanayin biyan kudin, yadda aka kashe kadaden sannan kuma sub a majalisa rahoto cikin makonni shida.

Wannan cigaban na daga cikin matakin da majalisar ke shirin dauka na hana kashe kudaden karshe na Abacha ba tare da amincewar majalisa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel