Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Saraki, Dogara, Kwankwaso, da wasu sun kafa ‘sabuwar APC’, suna shirin komawa PDP

Yanzu-yanzu: Saraki, Dogara, Kwankwaso, da wasu sun kafa ‘sabuwar APC’, suna shirin komawa PDP

Labarin da shigowa ba da dadewan nan ban a nuna cewa tsaffin mambobin ‘nPDP’ dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC), za su alanta fitarsu daga jam’iyyar domin sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugabannin kungiyar sun kunshi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahoto daga jihar Premium Times ya bayyana cewa wannan sabuwar kungiya za su shirya hira da manema labarai da yammacin yau Laraba domin alanta niyyarsu.

An sanyawa wannan sabuwar kungiyar ‘nAPC’ a matsayin mataki na farko na sauya shekansu domin fito-na-fito da shugaba Muhammadu Buhari.

KU KURANTA: Sojojin ruwan Najeriya sunyi nasarar lalata haramtattun matatun man fetir har guda 1500

Wannan ‘nAPC’ ya kunshi tsaffin gwamnoni, manyan yan majalisa da suke rikici da gwamnatin APC a yanzu.

Wasu daga cikin nPDP da ya kunshi shugaban majalisa Saraki; tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, Sanata Dino Melaye da ke fuskanta matsala da hukumomin tsaro.

Amma malam Buba Galadima ya ki bada cikakken bayanai kana bin. Yace : “Ban son inyi azarbabi.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel