Nigerian news All categories All tags
Ba kanta: Har yanzu bamu san yawan man feturin da ake sha a Najeriya ba - NNPC

Ba kanta: Har yanzu bamu san yawan man feturin da ake sha a Najeriya ba - NNPC

Babban kamfanin man Najeriya NNPC, a yau Laraba ta bayyana cewa har ila yau gwamnati bata san yawan man feturin da ake sha a Najeriya ba amma ta samar da wani hanya da za'a iya amfani da shi wajen gano yawan ainihin yawan man da yan Najeriya ke saya

Yayinda yake jawabi a taron baja kolin kamfanin mai da iskar na Najeriya, babban ma'aikacin hukumar, Mr. Henry Obih, yace majalisar zantarwan tarayya ta baiwa kamfanin NNPC aikin gano yawan man fetur.

Yawan man fetur da ake sha a Najeriya ya kasance abin tattaunawa a watannin da gabata, saboda hakan ne zai bada daman sanin kudinda NNPC ke samu da kuma kudin da take cirewa kafin sanya sauran a baitul-malin gwamnati, musamman yanzu da aka dawo biyan kudin tallafin mai.

Gabanin yanzu, NNPC ta ce ana shan litan mai miliyan 65. Hakan wai saboda ana hakan mai ganga miliyan 35 a rana sanadiyar masu fasa bututun mai suna sacewa kuma suna kafa gidajen man kansu a iyakokin Najeriya.

Amma gwamnonin jihohin Najeriya 36 suce wannan ikirari bogi ne kuma karya ne. Innama NNPC na amfani da shi wajen kin kai kudin da ya kamata baitul-malin gwamnati ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel