Nigerian news All categories All tags
Bincike ya nuna ashe kashi daya bisa dari na 'yan Najeriya ne ke karatu a jami'o'i

Bincike ya nuna ashe kashi daya bisa dari na 'yan Najeriya ne ke karatu a jami'o'i

- Karatun Jami'a ya zama sai dan sarki, saboda tsadarsa

- An gano kasa da mutum 2m ne ke karatun Jami'a

- Hukumar makarantu na jami'o'i NUC ce ta fidda kididdiga

Bincike ya nuna ashe kashi daya bisa dari na 'yan Najeriya ne ke

Bincike ya nuna ashe kashi daya bisa dari na 'yan Najeriya ne ke

Hukumar jami'o'i ta Najeriya tace kashi daya ne cikin dari na yan Najeriya ke samun shiga jami'o'i 164 dake fadin kasar.

Zababben sakataren hukumar, Abubakar Rasheed, yace haka a ranar talata yayin amsa tambayoyin yan jaridu a birnin Abuja.

Kamar yanda Mista Rasheed yace, jami'o'in kudi guda 75 na kasar suna samar da gurbin kashi 5.31 a cikin dari na daliban dake shiga jami'o'i a duk shekara a fadin kasar.

Yace wannan ba abun murna bane, domin kuwa akwai bukatar samar da jami'o'i ko kuma kara fadada wadanda ake dasu.

"Idan muka dubi yawan mutanen kasar mu, miliyan 198 kuma muka duba yawan mutanen dake samun shiga jami'o'i duk shekara, wanda basu miliyan 2 ba, zamu ga kashi daya ne tak cikin yawan mutanen kasar. Wanda kuwa ba abin murna bane."

DUBA WANNAN: Abunda muka tattauna da Atiku - Gumi

Yace abu ne mawuyaci ga kungiyar ta iya daidaita kudin makarantun kudi na kasar.

Gurin kuma kara wasu jami'o'in ko fadada wadanda ake dasu, dole ne ayi duba zuwa ga ingancin ilimin da za a dinga samu, cewar Adetokunbo Mumuni, daraktan SERAP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel