Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a daya daga cikin ma’aikatun tarayya

Gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a daya daga cikin ma’aikatun tarayya

Damuwa da matsalar karancin ruwa a wasu sassan kasar nan, gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a ma’aikatar ruwa domin bijiro da wasu hanyoyi da za a bi domin magance matsalar.

Gwamnatin ta bayyana cewar daya daga cikin matakan da zata dauka shine ta hada kai da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu da na aikin agaji domin cimma wannan manufa.

Ministan harkokin ruwa, Injiniya Suleiman Adamu, ya bayyana hakan jiya a Abuja, yayin wani taro na kasa da kasa a kan inganta samar da ruwa (NWSA) da aka gudanar jiya, Talata, a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a daya daga cikin ma’aikatun tarayya

Ministan harkokin ruwa; Suleiman Adamu

Adamu ya bayyana cewar, gwamnati zata kawo karshen matsalar karancin ruwa duk da ana samun yawaitar kwararowar jama’a daga kauyuka zuwa birane.

Ministan ya bayyana karfin gwuiwarsa cewar taron zai bayar da shawari masu amfani da zai taimakawa gwamnati wajen cimma burinta.

DUBA WANNAN: Kudin makamai: EFCC ta kwace Otal din N1bn da gidan N500m daga hannun wasu na kusa da Jonathan da Dasuki

A nasa bangaren, shugaban taron na NWSA, Dakta Eugene Pam, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewar taron zai samar da hanyoyin warware matsalar ruwa a Najeriya ta hanayar kawo masana da zasu taimakawa gwamnati da tsare-tsare da shawarwari masu amfani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel