Nigerian news All categories All tags
Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai

Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai

- Wani matashi maras tausayi ya kashe mahaifiyarsa har lahira

- Ya burma mata wuka ne har sau biyu da kuma nan take ta garzaya lahira

Wata babbar kotun majistire da ke Yaba a jihar Lagos ta bayar da umarnin cigaba da tsare wani mai suna Nuruddeen Bakare dan kimanin shekaru 37 a gidan yarin Ikoyi bisa zarginsa da dabawa mahaifiyarsa wuka, inda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai

Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai

Babbar mai shari'a na kotun majistiren Oluwatoyin Oghere ya bayar da Umarnin cigaba da tsare mai Laifin bisa Laifin da yayi na kasi. Ya kuma daga cigaban shari'ar har zuwa ranar 1 ga watan Augusta.

KU KARANTA: Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Tun da farko dai dan sanda mai gabatar da kara sajan Modupe Olaluwoye, ya bayyanawa kotun cewa wanda ake zargi da aikata Laifin, yayi laifin ne a ranar 6 ga watan Yunin da ya gabata akan titin Oremeji da ke unguwar Ilamasa Mushin.

Olaluwoye ya ce wanda ake zargin sun samu rashin jituwa ne da mahaifiyarsa mai kimanin shekaru 65 da haihuwa bisa mallakar kadara. Jim kadan da fara wannan takaddamar ne, sai Nuruddeen ya dabawa mahaifiyar ta sa wuka a wuyanta da kuma cikinta.

Wanda hakan ya sabawa sashi na 222 da kuma sashi na 223 kundin manyan laifuffuka na jihar Lagos.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel