Nigerian news All categories All tags
Tirkashi: Kotu ta bawa majalisa umurnin fara tsige shugaba Buhari

Tirkashi: Kotu ta bawa majalisa umurnin fara tsige shugaba Buhari

Kotun tarayya dake zamanta a Osogbo ta umurci majalisar tarayya ta fara shirye-shiryen tsige shugaba Muhammadu Buhari ba tare da bata lokaci ba.

Justice Maurina Adaobi Onyetenu ya bayar da wannan umurnin ne a yau Laraba sakamakon karar da wasu lauyoyi biyu suka shigar; Kanmi Ajibola da Suleiman Adeniyi inda suka bukaci kotun ta tursasawa wa majalisar tsige shugaba Buhari.

Wattani uku da suka gabata, lauyoyin biyu sun rubuta wasiku ga majalisar dattawa da wakilai inda suka bukaci a tsige shugaban kasar saboda zarginsa da su keyi da karya dokar kasa kuma su kayi barzanar zuwa kotu idan ba'a dauki mataki ba.

KU KARANTA: Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Sai dai yan majalisun basu dauki mataki a kai ba, hakan yasa lauyoyin suka garzaya babban kotun tarayya dake Osogbo inda suka bukaci kotun ta tursasa wa majalisun biyun tsige shugaban kasar.

In karar da suka shigar a ranar 19 ga watan Yunin 2018, sun bayyana dalilai hudu da yasa suke nema majalisar ta tsige shugaban kasan.

Laifufukan da suka tuhumar shugaban kasar da aikatwa sun hada da cewa

1) Shugaba Buhari ya yi takarar shugabancin kasa ba tare da ya mallaki takardun karatu da dokar kaza ta tanadar ga mai neman shugabancin kasa ba

2) Sunyi ikirarin shugaban kasar ya bawa hukumar INEC shedar kammala karatu na bogi

3) Sunyi ikirarin cewa shugaban kasar ya kasa kiyaye rayyuka da dukiyoyin 'yan Najeriya wanda shine aikinsa na farko a matsayin shugaban kasa

4) Sun kuma ce shugaban kasar ya saba kudin tsarin 1999 inda ya cire kudi har $496 miliyan na sayo jiragen yakin sama kirar Tucano ba tare da amincewar majalisar tarayya ba dai sauransu

Hakan yasa suke ganin ya dace majalisar ta tsige shugaban kasar.

Kotun da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Oktoban 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel