Nigerian news All categories All tags
Kama ka da hukumar DSS suka yi sadaukarwa ne ga dimokradiyyar Najeriya – Saraki ga Sanata Abaribe

Kama ka da hukumar DSS suka yi sadaukarwa ne ga dimokradiyyar Najeriya – Saraki ga Sanata Abaribe

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fadama Sanata Abaribe cewa ya kalli kama shi da aka yi a matsayin wani sadakarwa ga damokradiyya.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a lokacin da Abaribe yake bayyana yadda aka kama shi a kofar Hilton lokacin wani taro sannan aka kai shi gidansa domin bincike bayan an zarge shi da taimakawa a laifin kungiyar IPOB.

Da yake martani ga bayanin nasa, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa suna farin ciki da dawowar shi.

KU KARANTA KUMA: Wasu bebaye kuma kurame 2 sun auri junansu a Akwa Ibom (hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar yan sandan farin kaya (DSS) sun kama sanata mai wakiltan Abia ta kudi a majalisa, Eyinnaya Abaribe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel