Nigerian news All categories All tags
An kama iyaye biyu da suka yiwa da 'ya'yan cikinsu fyade

An kama iyaye biyu da suka yiwa da 'ya'yan cikinsu fyade

Sashen kare hakkin bil adama na hukumar yan sandan Najeriya ta tsare wasu iyaye maza biyu bisa laifin yin lalata da 'ya'yansu mata.

An kama Olawole Ibitoye mai shekaru 45 ne a unguwar Ketu na Epe bisa zarginsa da yin lalata da yarsa mai shekaru 14, yayin da shi kuma Ashiru Amusat mai shekaru 65 an kama shi ne bisa zarginsa da zagewa yarsa mai shekaru 12 a unguwar Shasha dake Egbeda.

An gano cewa Ibitoye ya fara lalata da yarsa ne tun tana da shekaru takwas a duniya kuma daga baya ya aurar da ita ga wani mutum mai suna Moses Okurukpe.

Karshen duniya: An kama iyaye biyu da suke lalata da 'ya'yan cikinsu a Legas

Karshen duniya: An kama iyaye biyu da suke lalata da 'ya'yan cikinsu a Legas

A yayin da yake gabatar dasu ga maneman labarai a hedkwatan yan sanda dake Abuja, kwamishinan yan sanda Imohimi Edgal ya ce an sanar da yan sandan lamarin ne saboda yarinyar ta dauki juna biyu.

Edgal ya ce an kai yarinyar gidan wasu masu maganin gargajiya inda ta kwashe kwanaki biyu tana nakuda kafin daga baya ta haihu amma abinda da haifa ya rasu.

Sai dai Ibitoye ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

Binciken yan sanda ya nuna cewa Amusat ya fara kwanciya da diyarsa ne bayan mahaifiyar yarinyar ta rabu dashi bayan ta haife ta. "Ta girma a wajen kakanta ne amma a watan Afrilun 2018, Amusat ya karbo ta daga hannun kakanta," inji kwamishinan yan sandan.

Kwamishinan yan sandan ya ce za'a gurfanar dasu a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

A bangarensa, Amusat ya ce shedan ne ya rinjaye shi ya kuma kara da cewa diyarsa ta amince da abinda ke faruwa tsakaninsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel