Nigerian news All categories All tags
An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Nuhu Gidado wanda ke aiki kuma a matsayin kwamishinan ilimi, ya yi umurnin rufe makarantar Sa’adu Zungur duka bangarorinta na sakandare da Firamare a babban birnin jihar.

An rufe makarantar ne bayan labarin kulla aure tsakanin manyan dalibai cikin sirri ya billo.

A cewar wata sanarwa daga mataimakinsa na musamman a kafar sadarwa, Yakubu Adamu, mataimakin gwamnan ya daura laifin wannan auren sirri da ake kullawa tsakanin dalibai a matsayin rashin da’a dake faruwa a gari.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wannan rashin da’a a tsakanin dalibai ya yawaita duk da cwar an raba ajujuwan mata da maza don daukar karatu.

An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

An rufe makarantarSakandare a Bauchi saboda kulla aure ba bisa ka’ida ba a tsakanin dalibai

An kuma bayyana cewa malaman makarantar sun gano hakan ne lokacin da daliban aji 2 na babban sakandare suka shirya liyafar biki irin wannan a harabar makarantar.

KU KARANTA KUMA: Makomar siyasar Igbo ya ta’allaka ne akan sake zabe na - Buhari

Hayaniyar wannan taro ne ya ja hankalin malamai inda suka yi gaggawan zuwa don ganin abun da ke faruwa sai suka ga cewa bikin aure ake yi.

Dalibi namijin ya biya sadakin N500 ga matar wacce itama daliba makarantar ce. Sannan sauran dalibai suka hada kudi aka siyi kayan motsa baki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel