Nigerian news All categories All tags
Ba zamu iya gyara lalatan da PDP tayi a shekaru 16 cikin shekara 3 ba - Oshiomhole

Ba zamu iya gyara lalatan da PDP tayi a shekaru 16 cikin shekara 3 ba - Oshiomhole

- Shugaan jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, yace jam’iyyarsa ba zata gushe tana sukar jam’iyyar PDP kan lalacewan abubuwa a Najeriya ba

- Ya ce APC ba zata iya gyara lalatan da PDP tayi cikin shekaru 16 ba cikin kankanin lokaci

- Oshiomhole ya ce an waye gari wasu da suka rike gwamnati a da suna rubuta wasikar borin kunya

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomole, ya ce jam’iyyarsa ba zata gushe tana sukar gwamnatin da ta shude na PDP ba kan lalatan da tayi na tsawon shekaru 16 a Najeriya.

Tashar Channels ta bada rahoton cewa Oshiomole, wanda yayi jawabi a taron gangami da nuna goyon baya ga shugaba Buhari na yankin kudu maso gabas da aka gudanar a Owerri, jihar Imo jiya Talata, 3 ga watan Yuli.

Ba zamu iya gyara lalatan da PDP tayi a shekaru 16 cikin shekara 3 ba - Oshiomhole

Ba zamu iya gyara lalatan da PDP tayi a shekaru 16 cikin shekara 3 ba - Oshiomhole

Ya soki jam’iyyar PDP da rashin aiwatar da ayyuka a yankin cikin shekaru 16 da suka kan karagar mulkin Najeriya.

Legit.ng ta tattaro cewa Adams Oshiomole ya ce an waye gar wasu da suke rike da gwamnati a shekarun baya sun fara rubuta wasiku.

KU KARANTA: Kwankwaso da Jama’an sa za su koma PDP domin ganin bayan APC

Wannan shine fitarsa na farko a matsayin shugaban jam’iyyar APC.

An rantsar da Adams Oshiomole a matsayin shugaban jam’iyyar ne ranan Lahadi, 24 ga watan Yuni 2018 a farfajiyar Eagle Square da ke Abuja bayan taron gangamin jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel