Nigerian news All categories All tags
El-Rufa’I ya samar da dokan da ka iya garkame yan Shi’a da wasu na shekara 7 a kurkuku

El-Rufa’I ya samar da dokan da ka iya garkame yan Shi’a da wasu na shekara 7 a kurkuku

Kungiyar yan uwa mabiya addinin Islam IMN wadanda akafi sani da mabiya kungiyar Shi’a da wasu yan sara-suka ko yan shara za su fuskanci fushin gwamnati na garkama a kurkuku har shekara 7, bisa ga sabuwar dokar da gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya samar.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a jihar Kaduna, Chris Umar, ya ce dokar haramta kungiyoyin na 2018 zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kuma wajabta bin doka da oda a jihar.

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta kungiyar mabiya addinin Shi’a, Sara-suka, Yan Shara da wasu kungiyoyin yan daba a jihar Kaduna a watan Oktoba, 2016.

El-Rufa’I ya bayar da umurnin garkame yan Shi’a da wasu na shekara 7 a kurkuku

El-Rufa’I ya bayar da umurnin garkame yan Shi’a da wasu na shekara 7 a kurkuku

Diraktan ladabtar da mutane a jihar Kaduna, Mr. Dari Bayero, ya ce gwamnatin jihar Kaduna na kan daukan matakai na kawo karshen kungiyoyi masu tada kura a cikin garin.

KU KARANTA: Kwankwaso da Jama’an sa za su koma PDP domin ganin bayan APC

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan kungiyar Shi’a sun hallaka jami’an dan sanda a wani rikici da ya barke tsakaninsu da yan sanda a Kaduna ranan da aka gurfanar da shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky, a babban kotun jihar Kaduna.

Yan kungiyar dai suna zanga-zanga ne kan cigaba da rike shugabansu tun shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel