Nigerian news All categories All tags
Makomar siyasar Igbo ya ta’allaka ne akan sake zabe na - Buhari

Makomar siyasar Igbo ya ta’allaka ne akan sake zabe na - Buhari

A jiya, Talata, 3 ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa makomar siyasan yan kabilar Igbo a Najeriya ya ta’allaka ne akan sake zabar sa a 2019.

Buhari ya bayyana hakan a babban taron APC na kudu maso gabas wanda aka gudanar a dakin wasar Dan Anyiam a jihar Imo, wanda gwamna Rochas Okorocha ya shirya.

Hakan ya kasance ne yayinda shahararrun shugabannin Igbo a APC na yankin kudu maso gabas suka yi biris da gangamin Okorocha.

Makomar siyasar Igbo ya ta’allaka ne akan sake zabe na - Buhari

Makomar siyasar Igbo ya ta’allaka ne akan sake zabe na - Buhari

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ministoci masu ci daga yankin, sanatoci masu ci daga yankin, tsoffin sanatoci, mambobin majalisar wakilai daga yankin duk sun ki halartan taron.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue

Haka zalika mataimakin gwamnan jihar, Eze Madumere, sanata Ifeanyi Araraume, tsoffin kakakin majalisar jihar, tsoffin kwamishinoni karkashin Okorocha da shugabannin APC sama da 150 a jihar sun yi biris da taron.

Shugaba Buhari ya ce yan Igbo ma na da damar neman mukami a siyasar kasar domin suma yan kasa ne, sannan ya sha alwashin mara masu baya idan lokacin yin hakan ya kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel