Nigerian news All categories All tags
Ya zama dole Buhari ya yi murabus idan har ba zai iya dakatar da kashe-kashe ba – Manyan limaman coci

Ya zama dole Buhari ya yi murabus idan har ba zai iya dakatar da kashe-kashe ba – Manyan limaman coci

Manyan limaman cocin Katolika na Najeriya (CBCN) sun sake gabatar da bukatarsu na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus kan kashe-kashenda ake yi a fadin kasar.

Da suke martani akan wani hari da aka kai kan wasu masu bauta a wani cocin jihar Benue, kungiyar ta CBCN sun zargi shugaba Buhari ya yin watsi da hakkin da kundin tsarin mulki tad aura mashi na tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’umma a Najeriya sannan suka bukaci yayi murabus.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kungiyar CBCN sun ce sun sake neman shugaba Buhari yayi murabus ne saboda fadar shugaban kasa ta basar da lamarin da kungiyar tayi korafi akai a baya.

Ya zama dole Buhari ya yi murabus idan har ba zai iya dakatar da kashe-kashe ba – Manyan limaman coci

Ya zama dole Buhari ya yi murabus idan har ba zai iya dakatar da kashe-kashe ba – Manyan limaman coci

Wannan sabuwar bukata da kungiyar ta nema martani ne ga kashe-kashen da akayiwa wasu mutane a garin Jos.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue

Kashe-kashen wanda shugaba Buhari yayi Allah wadai das hi ya janyo cece-kuce da dama inda ake ta sukar gwamnati, tare da lauyoyi da hukumomin kare hakkin dan adam ke kira ga a dauki mataki sannan kuma suka yi barazanar shigar da shugaban kasar kara.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana cewa kashe-kashen baida alaka da wani lamari na addini ya bayar da tallafin naira biliyan 10 ga garuruwan da abun ya shafa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel