Nigerian news All categories All tags
Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Hukumar fasa kwabri na kasa Kwastam ta kama wasu motocci dauke da shinkafar kasashen waje a titunan Kaduna da Zaria da Kano kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Mataimakin Comptroller kuma kwamandan rundunar, Ekanem Wills ne ya tabbatar da kamun yayin da yake hira da manema labarai a ranar Litinin a Kaduna. "Munyi nasarar kama motocci kirar Golf wagon takwas da J5 uku wanda ke dauke da buhunan shinkafar da aka shigo dasu ta barauniyar hanya," inji shi.

KU KARANTA: Kisan jigo a jam'iyyar APC: 'Yan sanda sun kama mutane 5, duba sunayensu

Mr Wills ya cigaba da bayanin cewa kowanne mota na dauke da a kalla buhuna 40 - 45 na shinkafa. Ya kuma ce hukumar ta tsare mutanen da aka kama dauke da shinkafar yayin da ake cigaba da zurfafa bincike.

Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje

Ya ce gwamnati ta samarwa rundunar sabbin motoccin sintiri saboda a karfafa wa jami'an hukumar gwiwa wajen kawo karshen mummunar sana'ar shigo da haramtatun kayayaki Najeriya.

Ya tabbatar da cewa rundunar zata kwace dukkan kayayakin da ake shigowa dasu Najeriya ta haramtattun hanyoyi kana ya gargadi masu wannan mummunan sana'ar su tuba su canja wata sana'ar.

Wannan lamarin ya afku ne makonni kadan bayan gwamnatin tarayya ta sanar cewa zata kule iyakan Najeriya da wasu kasashen da ke makwabtaka da ita saboda kiyaye shigo da kayayaki ta haramtatun hanya.

Ministan Noma da raya karkara, Aude Ogbeh ne ya bayar da wannan sanarwan a yayin da yake jawabi a wata taron wayar da matasa kan shugabanci da Guardians of the Nation International ta shirya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel